<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Sabuwar Urushalima amaryar Yesu ce,
 Mai sheƙi kamar rana, ko haske kuwa gani.
 Ƙofofi na daraja, hanyar zinariya,
 A cikinta ga kogi da itace na rai.

[V2]
 2) In kai ga wannan birni wurin da hawaye,
 La'ana, bakinciki, duka sun shusshude.
 Ko mutuwa da kanta an ci nasararta.
 Da Ɗan Rago da Uba ɗaukakar birni ne.

[V3]
 3) In yi sujada tare da sauran tsarkaka.
 Sa rera, Halleluya, in haɗa muryata. Kullum in yi mamaki yadda zunubaina
 Ta wurin jinin Yesu, Allah ya gafarta.</lyrics>
<title>Sabuwar Urushalima Amaryar Yesu Ce LW320</title>
<hymn_number>320</hymn_number>
</song>